Monday 20 October 2025 - 09:09
Aikin makarantar hauza da jami'a shi ne kawar da jahilcin dake cikin al'umma

Labaran hauza / Mai girma Ayatullahi Jawwadi Amoli ya fayyace cewa: duk mutmenda ya yi sakaci, kuma yayi aiki ba tare da tunani ba, ba zai amfana da komai ba sai da nadama, wanda kuma ya tsaya tsayin daka,  yana mai hangen nesa, mai tunani zai samu aminci da nasara.

Kamfanin dillancin labaran Hawza ya labarta cewa, a yau Laraba ne aka gudanar da zaman darasin kyautata ɗabi'u da ɗa'a na mako-mako na Ayatollah Jawwadi Amuli, a masallacin A'azam dake birnin Qum, tare da halartar bangarori daban-daban na al'ummar ƙasar.

Mai girman ya ci gaba da bayani akan gajejjerun lafazzan Nahjul Balagha, yana mai ishara da fitacciyar kalma ta 181 ta Amirul Muminin (as), ya ce: Imam yana cewa a cikin wannan hikimar:
" 'Thanara" (Abin girba daga) sakaci shine nadama, kuma '"Thamarar"  azama da hangen nesa shine aminci." Kada mutum ya yi wani abu ba tare da tunani, tsarawa, da hangen nesa ba, domin halaye da aiyukan sa na ƙashein kan sa a keɓe suna da alaƙa da al'umma, kuma kowane yanke shawara na kansa zai yi tasiri ga tsarin zamantakewa.

Ayatullah Jawwadi Amuli ya ci gaba da cewa: Hankali "Nazari" na ƙa'ida yana da alhakin tunani da kuma bambance daidai da kuskure, ahalin da hankali "Amali" na zahiri yana da alhakin yanke hukunci da nuna azama; kuma waɗannan tsare-tsare guda biyu sun bambanta da juna, kuma kawai ruhi mai ƙarfi, ruhin ɗan adam, da bangaskiyar Allahntaka su ne ke daidaita waɗannan ikon guda biyu (Nazari da aiki", don hanyar rayuwar ɗan adam ta tafi daidai.

Sai wannan Marja'in na Taƙalidi ya ce: 
Jihadin ciki shi ne mutum ya gano ƙarfin iko na dakarunsa na ciki, ya fahimci aikin kowannensu, ya kuma daidaita tsakanin su, ta yadda zai iya yanke hukunci mai kyau don yin aiki na ƙwarai.

Aikin da ake aiwatarwa a fagen Hauza da Jami'a; 
a Hauza ana amfani da hankali "nazari", na ƙa'ida, wanda manufarsa ita ce kawar da jahilci da buɗe fuskar ilimi, amma aikin malaman tarbiyya da gyaran zamantakewa, yana kan ƙa'idar aiki da hankali "Amali" ne, na Zahiri, wanda hadafin sa shi ne, kawar da "Jahala" wauta";

 Ita "Jahala" wauta, tana bayyana ne a fagen yanke shawara da aikata managartan halaye; kamar gudanar da al'umma da rayuwa ta yau da kullum; a yayin da shi kuma "Jahal" jahilci, yana da alaƙa da rashin sani ne a fagen Ilimi.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da ruwaya mai haskakawa da take cewa; “Sau daywa ana samun mai ilimin da Jahilcinsa ne ya kashe shi, alhali iliminsa yana tare da shi bai amfanar da shi da komai ba,” ya kara da cewa: “Mutane da yawa suna da ilimin kimiyya, amma a aikace suna fama da "jahala", wauta, kuma ba sa yin aiki da hikima da hankali wajen yanke hukunci da Shawara.

Don haka dole ne mutum ya rayu ta yadda cibiyar yanke shawara ta cikin gida zata yi aiki bisa ga hankali da tsoron Allah, kuma yanke shawarar sa ma ya zama yana bin bayan (hankali da ilimin) na kaḍai; ilimi shi kaɗai baya isa; da yawa daga cikin masu ilimi, sun faɗa tarkon wauta da miyagun ɗabi'u da gurɓatattun halaye, a sakamakon rasa hankalin aiki, da yenke shawara dai-dai.

Haka nan kuma yayin da yake ishara da hikimomin littafin Nahj al-Balagha hikima ta 48, babban Malamin ya bayyana cewa, ana samun nasara a cikin al'amuran ɗaiɗaiku da na al'umma ne - a zamantakewa yayin da aka gina yenke shawrwari, tattarawa da nazartar ra'ayoyi akan kyakkyawan tunani. Sannan shi kuma ingantaccen tunanin ya ginu kan kakkangewa da boye sirri.

A ƙarshe Ayatullah Jawwadi Amuþli ya tunatar da cewa: "Duk mutmenda ya yi sakaci, kuma yayi aiki ba tare da tunani ba, ba zai amfana da komai ba sai da nadama, wanda kuma ya tsaya tsayin daka,  yana mai hangen nesa, mai tunani zai samu aminci da nasara."

Tags

Your Comment

You are replying to: .
captcha